Tinubu ya umarci dukkan ma’aikatan gwamnati da suka koma kasashen ketare da aiki da su dawo da albashin da sukaci a baya

0 187

aa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci dukkan ma’aikatan gwamnati da suka koma kasashen ketare da aiki da su dawo da albashin da suke ci gaba da karba zuwa lalitar gwamnati.

Shugaban kasa ya bayar da umarnin a hakunta masu sanya idanu da shugabannin hakumomi bisa tuhumar taimakawa wajen aikata laifi a karkashin kulawar su.

Tinubu ya bayar da wannan umarni ne jiya a wajen wata liyafa da ofishin shugaban ma’aikata na kasa ya shirya domin karrama makon aikin gwamnati na bana.

Yayin taron an kuma karrama wasu ma’aikata.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin sakataren gidan gwamnati sanata George Akume, ya bayyana bacin ransa ga ayyukan ma’aikatan na bogi.

Ya jaddada cewa gwamnati zata dauki matakan da suka dace domin tabbatar da hakunta su, da kuma dawo da kudaden da suka karba zuwa lalitar gwamnati.

Shugaban ya kuma jinjina irin kalubalen da ke tattare a harkar aikin gwamnati, yana mai cewa gwamnati zata tabbatar ta warware su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: