Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsawaita wa’adin shugabancin shugabar hukumar shigi da fici ta kasaa, Kemi Nandap.
Nandap ta fara aiki ne a hukumar a ranar 9 ga Oktoban 1989.
Tinubu ya naɗa ta shugabar hukumar ne wato kwantura-janar a ranar 1 ga Maris na shekarar 2024, domin ta jagoranci hukumar zuwa ranar 31 ga Agustan 2025.
Amma a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce saboda nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Nadap ne ya sa shugaban ƙasar ya tsawaita shugabancinta zuwa 31 ga Disamban 2026.
Ya ce a ƙarƙashin jagorancinta an samu ci gaba da dama, musamman wajen zamanantar da ayyukan hukumar da tabbatar da kula da iyakokin ƙasar.