Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a jiya tabbatar wa da Libya cewar Najeriya na tare dasu da kuma nuna alhini a wannan mayuwacin hali da kasar ta shiga sakamakon ambayiyar ruwa.
A wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar ya jajantawa iyalan da suka rasa yan uwansu a ambaliyar da ya bayyana da annoba.
Yace abin damuwa ne rasa rayuka, da muhallai da kuma asarar dukiyoyi.
Ya kara da cewa Najeriya a shirye take ta bayar da duk wata gudunmawa da goyon baya da ake bukata domin taimakawa mutanen kasar da ibtila’in ya shafa.
Haka kuma majalisar kolin harkokin addinin musulunci ta kasa tace ibtila’in ya aukawa mutanen kasar yayin da al’uma basu gama murmurewa daga girgizar kasa data auku a Moroko ba. Mataimakin babban sakatare na majalisar farfesa Salisu Shehu yace majalisar ta roki al’umar Najeriya da na duniya, da hakumomin bayar da agaji, gwamnatoci da sauran kungiyoyi da dai-daikun mutane da su taimakawa mutanen da ambaliyar ta shafa.