Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya buƙaci jagororin yankin Naija Delta su shawarci gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya yi biyayya ga hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar kan rikicin siyasar jihar.
Yayin da yake jawabi da masu ruwa da tsaki na yankin kudu maso kudancin ƙasar, ƙarƙashin ƙungiyar ci gaban yankin Naija Delta a fadarsa da ke Villa ranar Talata, shugaba Tinubu ya ce ya ɗora alhakin samar da zaman lafiyar jihar River a wuyan jagororin ƙungiyar.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sadaukarwar jagororin yankin wajen ganin jihar ta yi aiki da kundin tarin mulkin ƙasar, ta hanyar yin biyayya ga dokokin ƙasar don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
”Mutunta ɓangaren shari’a muhimmin ɓangare ne a tsarin dimokraɗiyya,” kamar yadda shugaban ƙasar ya ya bayyana, cikin sanarwar da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar.
Ya ƙara da cewa ”Wannan ƙasa ce da ake amfani da dokokin na shari’a, inda babu waɗannan dokoki, da ban zama shugaban ƙasa ba, na yi imani da tsarin dimokraɗiyyarmu, muna da fata mai kyau. Ɗan’adam kan yi kuskure, amma idan kotu ta yanke hukunci to zance ya ƙare”, a cewar shugaban ƙasar.
“Don haka ina roƙonku, ku koma gida ku taimaka a yi amfani da hukunci kotu cikin ƙanƙanin lokaci, na ɗora alhakin a kanku, ku taimaka ku shiga tsakani a sirrance da kuma zahiri ku shawarci gwamna, a rungumi hanyar zaman lafiya da kwanciyar hankali”, a cewar Shugaba Tinubu.
A kwanakin baya ne dai kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar tare da mayar da ƴanmajalisar jihar 27 da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ma hamayya a jihar, wani abu da bai yi wa gwamnan jihar daɗi ba.
Kodayake cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar bayan yanke hukuncin gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta bai wa hukumar zaɓen jihar goyon bayan sake shirya wani zaɓen ƙananan hukumomin.