Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Mai Shari’a Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun domin kama aiki a matsayin babbar mai shari’a ta ƙasa a ranar Litinin bayan Majalisar Dattawa ta amince da naɗin nata.
Ita ce mace ta biyu da take riƙe muƙamin a tarihi, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.
An yi bikin rantsuwar ne a gaban tsofaffin manyan alƙalai huɗu, ciki har da mace ta farko da ta riƙe muƙamin Mariam Aloma Mukhtar.
“Fannin shari’a babban ginshiƙi ne da ke tallafe da tsarin dimokuɗaiyarmu, kuma tsawon shekaru fannin shari’ar Najeriya ya sha nuna tasirinsa na mai shiga tsakani domin tabbatar kowa ya bi doka,” a cewar Shugaba Tinubu yayin taron.
“Matsayinki na zama wuri na ƙarshe da talaka zai samu adalci yana da muhimmanci wajen saka wa mutane ƙwarin gwiwa kan dimokuraɗiyya,” in ji shi.