Tinubu ya jajantawa iyayen da iyalan wadanda suka rasu sanadiyyar iftila’in gobara a jihar Zamfara

0 94

Shugaban kasa Bola Tinubu a jiya, ya jajantawa iyayen da iyalan wadanda suka rasa rayukan su a wani iftila’in gobara da ya faru a wata makarantar almajirai dake kaurar Namoda a jihar Zamfara.

Tinubu ya ake da sakon ta’aziyyar ne a cikin wani bayani mai dauke da sa hannun mataimakin sa na musamman akan yada labarai da tsare-tsare Bayo Onanuga.

Wutar dai wadda ta tashi a makarantar tsangayar ta lakume rayuka 17 da kuma raunata wasu yaran 15.

Rundunar yan sandan jihar Zamfara dai ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace kimanin yara 17 bakwai suka rasa rayukan su, wasu 15 kuma suka jikkata yayin faruwar lamarin.

Kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Shehu Dalijan, yace wutar ta soma tashi ne daga 2 na daren ranar laraba saboda kona wasu kara na Masara, inda ta fantsama izuwa ga rufin makarantar yayin da daliban ke bacci.

Leave a Reply