Shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na tallafa wa bunkasa jami’o’i, musamman wajen samar da damammaki domin cika aikinsu na jagorantar fannin makamashi.
A yayin bikin yaye dalibai karo na hudu a Jami’ar FUPRE da ke Effurun a Jihar Delta, shugaban ya bukaci hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jami’ar domin mayar da ita cibiyar fasaha ta duniya a bangaren ilimin makamashi.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Maritime ta Najeriya, Farfesa Emmanuel Adigio, wanda ya wakilci shugaban kasar, ya jaddada cewa matasa na da rawar da zasu takawa wajen kirkire-kirkiren fasahohin da za su samar da mafita mai dorewa ga Najeriya da ma Afirka baki daya.
A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar, Farfesa Akpofure Rim-Rukeh, ya bayyana cewa bikin ya kasance na kammala wa’adinsa na shekaru biyar, inda aka yaye dalibai 3,369 wadanda suka hada da masu digiri na farko 2,683 da kuma masu digiri na biyu da na uku su 686, yayin da dalibai 51 suka samu nasarar kammala digiri na farko da daraja ta daya.