Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su sauya tunaninsu akan kasar

0 153

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su sauya tunaninsu a kan kasar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaban dai na magana ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga majalisar dokokin ƙasar waɗanda suka kai masa ziyarar barka da sallah,.

Mista Tinubu ya ce “lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su sauya hali da tunaninsu ga Najeriya domin ciyar da ƙasar gaba”.

“Yan ƙasa da ke yawon neman wayar lantarki domin su cire da tuge titin dogo da dai sauran ayyukan ɓaagari, E, na amince akwai talauci, akwai wahalhalu. Amma ba mu kaɗai ne mutanen da muke shan wahala ba. Dole ne mu tunkari kalubalen da ke gabanmu.” In ji Tinubu.

Ya ƙara da cewa “akwai bukatar wasu ƴan ƙasar su sauya tunaninsu su kuma zama masu taimakawa wajen warware ƙalubalen da tattalin arziƙin ƙasar ke fuskanta. Saboda haka akwai buƙatar daina fasaƙwauri da cin dunduniyar tattalin arziƙin.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: