Tinubu ya bayar da umarnin sake duba shirin biyan N8,000 ga talakawan Najeriya

0 293

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin sake duba shirin gwamnatinsa na biyan Naira dubu 8,000 duk wata ga talakawan kasar miliyan 12 na tsawon watanni shida, a wani mataki na dakile illolin cire tallafin man fetur.

Shirin na kunshe ne a cikin wata wasika da aka karanta a ranar Alhamis din da ta gabata a zauren majalisar wakilai dangane da neman lamunin dala miliyan 800 da gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta yi na shirin samar da tsaro na zamantakewar al’umma.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, a cikin wata sanarwa a jiya talata, ya lura cewa shirin ba shine kawai abu a cikin kunshin tallafin da Tinubu ya kaddamar ba.

Alake ya ce shugaban kasar ya sha alwashin sanya ‘yan Najeriya a cikin manufofin shirin gwamnatinsa. A cewarsa, Tinubu ya ba da umarnin a sake duba tsarin tallafi na dubu 8,000 da aka shirya domin tallafawa masu karamin karfi ga mafi yawan gidaje da gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: