Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bada Naira dubu hamsin-hamsin ga iyalai miliyan 3.6 har tsawon wata uku a faɗin Nijeriya.
Wannan na ɗaya daga cikin yarjejeniyoyi da aka cimma a ganawar da Tinubu ya yi da gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan a yau Alhamis a Abuja.
Shugaban ya bada umarnin raba kuɗin ga iyalai dubu 100 a ko wacce jiha har na tsawon watanni uku.
Sauran batutuwa da aka cimma a ganawar sun hada da:
Bawa iyalai 100,000 a kowace jiha tallafin N50,000 na tsahon wata uku.
* Ware Naira biliyan 155 domin siyen kayan abinci da za a tallafawa masu ƙaramin ƙarfi kan farashi mai rahusa.
* Baiwa kowace jiha Naira biliyan 10 domin sayen motocin sufuri masu aiki da iska gas domin sauko da farashin kuɗin zirga-zirga.
* Gaggauta fara aikin hanyar da ta tashi daga Sakkwato zuwa Badagary a Lagos. Hanyar zata ratsa ƙauyuka kimanin 216, madatsun ruwa (dams) guda 58, ƙananan hukumomi 156 da manyan garuruwa 39 da kuma gonaki da suka kai kimanin hectare miliyan ɗaya. Titin zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Niger da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Lagos.
* Shugaba Tinubu ya kuma amince da biyan kuɗin aikin hanyar jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri wadda za ta ratsa jihohin Rivers da Abia da Enugu da Benue da Nasarawa da Plateau da Bauchi da Gombe da Yobe da kuma Borno.
* Haka nan an amince da biyan kuɗin da ake buƙatar domin yin aikin hanyar jirgin ƙasa da ta taso daga Ibadan zuwa Abuja a wani ɓangare na aikin dogo da ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Aikin zai haɗa jihohin Lagos da Ogun da Oyo da Osun da Kwara da Niger da Abuja da Kaduna da kuma Kano.
* Shugaban ƙasa ya kuma bada umarnin cigaba da aikin hanyar Lagos zuwa Calabar wadda kuma zata yi rassa a jihohin Benue da Kogi da Abuja da Nasarawa da Enugu da Ebonyi.