Tinubu ya amince da kudi Naira Bilyan 2 a matsayin kudin tallafi ga babban birnin tarayya Abuja

0 307

Ministan Babban Birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kudi Naira Bilyan 2 a matsayin kudin tallafi ga babban birnin tarayya Abuja.

Nyesom Wike wanda ya bayyana haka jiya yayin da yake ganawa da yan kwangila a ofishin sa, bayan an kammala zaman majalisar zartarwa jiya.

Ministan ya tabbatar da samun kudin Naira Bilyan Biyu daga shugaban kasa domin rabawa mazauna Abuja a matsayin rage radadin halin da ake ciki,sannan kuma ya ce kudin za’a yi amfani da su wajen magance kalubalan tafiye-tafiye.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya na duba yuyuwar kara kudaden ayyuka,sannan ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja zata maida hankali wajen tattara kudaden haraji.

Kazalika ya kuma gargadi yan kwangila cewa babu batun bada uzuri akan abinda ya shafi aiki.

Gwamnatin Tarayya ta amincewa gwamnatocin Jihohi 36 ciki hadda babban birnin tarayya Abuja domin ragewa al’umomin su radadin cire tallafin man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: