Tinubu ne kadai zai iya samar da tsayayyir wutar lantarki a Najeriya

0 227

Kwamatin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyar APC, ya ce akwai damar samar da wadatacciyar wutar lantarki da kuma shirin samar da gidaje ga yan Najeriya cikin shekarar 2023.

Kakakin Kwamatin Yakin Neman Zaben Mista Bayo Onanuga, shine ya bayyana hakan cikin wata wasikar barka da sabuwar shekara ga yan Najeriya wanda ya rabawa manema labarai a Abuja.

Da ya juya bangaren zaben 2023, Kwamatin Yakin Neman Zaben ya ce zaben yana da matukar muhimmanci ga kasar nan, inda ya kara da cewa dole ne yan Najeriya su fita suka zabi wanda suke so.

Kwamatin ya ce bukaci yan Najeriya da kada su sayar da yan cin su, ta hanyar sayar da katin zaben su saboda kudi.

Sanarwar ta ce yin zabe abune da ya rataya a wuyan yan kasa wanda hakan ne zai basu damar zaben mutumin da suka aminta dashi wajen ciyar da kasar nan gaba.

Haka kuma Kwamatin ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi Jam’iyar APC a matakai daban-daban domin cigaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: