Tawagar ‘yanwasan Kano Pillars ta yi hatsarin mota

0 184

Tawagar ‘yanwasan ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta yi hatsari a kan hanyarsu ta zuwa birnin Jos na jihar Filato.

Ƙungiyar ta ‘yan ƙasa da shekara 19 ta tafi Jos ne domin buga wasan mako na biyar da Plateau U-19 a gasar matasa.

“‘Yanwasa da yawa da kuma direban motar sun ji raunuka a hatsarin kuma nan take aka kai su asibiti,” a cewar wani saƙo da ƙiungiyar ta wallafa a shafinta na X.

Ta ƙara da cewa “cikin sa’a babu wanda ya rasu kuma tawagar likitoci na ci gaba da saka ido”.

  • BBC Hausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: