Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yace tattaunawa da barayi ‘yan bindiga ita ce hanya mafi dacewa wajen dorewar zaman lafiya a jihar, inda yace baya dana sanin kasancewar gwamnatinsa ta bi wannan hanyar.
Matawalle ya fadi haka daidai lokacin da ake ta tofa albarkacin bakuna akan ingancin hanyoyin da ake bi wajen magance matsalar tsaro da ta ki ci, ta ki cinyewa a Arewa maso Yamma.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Yace duk da tarin sojojin da aka kawo da kuma luguden wutar da ake ta yiwa barayi babu kakkautawa, karkashin gwamnatinsa, kashe-kashen barayi yan bindiga na cigaba da karuwa a wani lamari mai firgitarwa.