Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar yayi tsinkayen cewa shirin tallafawa jama’a na Gwamnatin Buhari, shine wanda yafi kowanne a duniya.
Gwamnan ya sanar da haka a garin Gagarawa wajen kaddamar da shirin a karin kananan hukumomi goma sha takwas na jihar.
Yace wadanda ke sukar Gwamnati, masu fada aji ne sosai, wadanda basu da matsala idan komai ya lalace, domin su samu damar cigaba da wadaka da dukiyar jama’a ido rufe.
- An sace wasu mata biyu malaman coci a jihar Anambra
- Gwamnatin jihar Jigawa na ci gaba da biyan hakkokin wadanda sukayi ritaya
- An nada Farfesa Abubakar Jika Jiddere a matsayin kakakin kungiyar dattawan Arewa
- Wadanda ke rike da akalar gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Solomon Dalung
- An kashe sojin Najeriya 6 a jihar Borno
Gwamnan yace jihar ce kan gaba wajen yawan mutanen da ke cin gajiyar shirin, inda aka biya naira biliyan tara da miliyan saba’in da hudu ga mutane dubu ashirin da shida da dari bakwai da talatin da hudu, tsakanin watan Augustan 2017 zuwa Aprilun bana.
Yayi bayanin cewa an kaddamar ne domin mutane dubu ashirin da shida da dari bakwai da talatin da hudu, yayin da aka zabi karin mutane dubu talatin da daya da dari tara da arba’in da tara domin biyansu kudaden wata-wata a karkashin shirin.