Tafiyar Gwamna Ganduje zuwa ƙasar Amurka domin halartar wani kwas ta jawo ce-ce-ku-ce

0 330

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tafi kasar Amurka domin halartar wani kwas na tsawon mako guda a jami’ar Harvard.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar, ta ce gwamna Ganduje na halartar kwas kan inganta jagoranci na kwarai a makarantar kasuwanci ta jami’ar Harvard da ke birnin Boston.

Ya ce gwamnan ya mika mulki tare da bai wa mataimakin gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna cikakken ikon zama mukaddashin gwamnan jihar.

Sanarwar ta kara da cewa duk wata hada-hadar gwamnati daga yanzu za a aikata zuwa ofishin mataimakin gwamna domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: