Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda da masu tayar da kayar baya 42 tare da kama 41 yayin kubutar da mutum 93
Helikwatar tsaro ta sanar da cewa sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda da masu tayar da kayar baya 42, tare da kama 41 yayinda aka kubutar da mutane 93 da akayi Garkuwa da su cikin makonni biyu da suka gabata.
Mukaddashin daraktan yada labaran ayyukan tsaro, Bernard Onyeuko ya bayyana cewa an gudanar da ayyukan ne a yankunan arewa maso gabas, arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.
Ya bayyana cewa rundunar Operation Hadin kai ta kashe yan Boko Haram 16, tare da kama wasu 29 yayin da ta kubutar da fararan hula 40 a arewa maso gabas.
Mukaddashin ya kara da cewa rundunar operation Hadarin Daji a yankin arewa maso yamma, ta kashe sama da yan bindiga 14, tare da kama wasu 24 yayinda ta kubutar da mutane 36 da ayyukan ta’addancin ya rutsa da su a yankuna daban daban.
Kakakin helikwatar tsaron yayi bayanin cewa an kwato bindiga kirar AK47 guda 7, sai babura 6, da kayan sojoji da na yan sanda na bogi, da motoci 6 da sauran wasu kayayyakin da aka kwato a tsakanin kwanakin.
Haka kuma ya bayyana cewa rundunar safe Haven ta gudanar da ayyuka da dama a yankuna daban da suka hada da Jihar Pleteau, Bauchi da kuma Kaduna a tsakanin kwanakin.