Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda biyu a jihar Taraba
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar jiya.
Ya ce sun kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara. Ya kuma ce sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu, da da harsashi na musamman guda 56.