Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun bayyana kawo ƙarshen ɗaurin talalar da suke yi wa hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo, suna masu cewa a yanzu yana da damar barin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin, Kanal Ulrich Manfoumbi, sojojin suka karanta a gidan talbijin na ƙasar ranar Laraba da maraice, ya ce an saki Ali Bongo ne bisa dalilai na rashin lafiya.
“A yanzu, idan ya ga dama yana iya fita daga ƙasar domin a duba lafiyarsa,” in ji sanarwar.
Tun bayan da sojojin suka kifar da gwamnatin Ali Bongo ranar 30 ga watan Agusta ne suka ci gaba da tsare a gidansa.
Matakin sakin hamɓararren shugaban ƙasar na zuwa ne bayan da sojojin suke ta samun matsin lamba daga ƙungiyar ƙasashen tsakiyar Afirka da ECCAS da kuma maƙwabtan ƙasar na cewa su martaba lafiya tare da mutunta hamɓararren shugaban ƙasar
A shekarar 2018 ne dai, Ali Bongo ya gamu da cutar shanyewar ɓarin jiki. Yanayin lafiyarsa ya kasance abin damuwa musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe.