Sojojin dake mulkin Guinea sun umarci bankuna da su rufe asusun dake da alaka da gwamnati

0 223

Sojojin dake mulkin Guinea sun umarci bankuna da su rufe dukkan asusun dake da alaka da gwamnati domin alkinta dukiyar kasa.

Sojojin wadanda suka kwace mulki a karshen makon da ya gabata, sun ce umarnin ya shafi asusun hukumomin da na daidaikun mutanen da ke shirin barin gwamnati.

Manyan jami’an tubabben shugaban kasa Alpha Conde, baza su samu damar hulda da asusunsu ba.

Shugabannin juyin mulkin sun kwace iko a ranar Lahadi kuma sun ce suna so su kawo karshen yawaitar rashawa da cin zarafin bil’adama da shugabanci mara kan gado.

Kungiyar cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), wacce take so a koma bin doka da oda, ta shirya wata tawaga da zata tattauna da hukumomin kasar ta Guinea.

Kungiyar ta ECOWAS ta kuma yi kiran da aka saki Shugaba Alpha Conde wanda sojoji suke rike da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: