Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 185 tare da kama 212 a cikin makon da ya gabata

0 209

Hedikwatar tsaron kasa ta koka kan yadda yawaitar sace-sacen mutane a fadin kasar nan ya mamaye nasarorin da sojoji ke samu a kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa.

Daraktan yada labarai na Hedikwatar tsaro na kasar nan, Manjo Janar Buba Edward ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau basabar.

Buba ya ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 185 tare da kama 212 a cikin makon da ya gabata. Ya kuma ce an ceto ‘yan kasar nan 71 wadanda da aka sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: