Sojoji sun kashe mayaka sama da 120 na Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas
Helkwatar tsaro tace dakarun operation Hadin Kai sun kashe mayaka sama da 120 na Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas cikin makonni uku da suka gabata.
Daraktan Yada Labarai na Helkwatar Tsaro, Bernard Onyeaku, ya sanar da haka yayinda yake bayyana cigaban da aka samu a ayyukan sojoji a fadin kasarnan tsakanin ranar 20 ga watan Janairu zuwa watan Fabrairu da muke ciki a Abuja.
Onyeaku yace a lokacin luguden wuta ta sama da ta kasa, an kashe kwamandojin ISWAP da Amir din su cikin har da mayakan kasashen waje wadanda suke hada bama-bamai.
Ya kuma ce mayaka 965 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a gurare daban-daban cikin makonnin.
Onyeaku yace mutane 104 daga cikin mayakan da suka mika wuya, ‘yan kungiyar ISWAP ne, yayin da aka ceto mutane 25 da aka sace.