Sojin Najeriya sun farmaki wani sansanin ‘yan bindiga a jihar Taraba

0 102

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kai farmaki wani sansanin ‘yan bindiga a yankin Angwan Bala da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

A yayin farmakin, an kashe daya daga cikin ‘yan bindigar, yayin da aka kama mutum 23, ciki har da mata hudu.

Sojojin sun kwato makamai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47 guda hudu, alburusai 80, da kuma babura 16.

Kwamandan Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya ce wannan farmakin alama ce ta jajircewar sojojin wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga a yankin.

Leave a Reply