Sojin Najeriya na samun gagarumin ci gaba wajen yaki da satar man fetur a yankin Neja Delta

0 47

Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa rundunar sojin na samun gagarumin ci gaba wajen yaki da satar mai da fasa bututun mai a yankin Neja Delta.

Oluyede ya jaddada cewa karuwar yawan man da ake hakowa a kasa shaida ce karara kan nasarorin da ake samu a wannan muhimmin yaki da zagon kasa ga tattalin arziki.

Oluyede, wanda ya samu wakilcin kwamandan rundunar horaswa da koyarwa ta sojojin, Manjo Janar Kevin Aligbe, ya bayyana hakan yayin wani liyafar cin abincin Kirsimeti tare da sojojin na shiyya ta 6 a Fatakwal. Ya bukaci hadin kan al’umomi don baiwa sojoji damar samun gagarumar nasara a yakin da ake yi da satar mai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: