Sojin mulkin Nijar sun katse wutar lantarki da ruwan sha ga ofishin jakadancin Faransa

0 308

Rundunar sojan Nijar ta katse wutar lantarki da ruwan sha ga ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai ba tare da izinin isar da abinci ba kamar yadda kafar yada labarai ta Turkiyya Anadolu ta ruwaito, ta nakalto majiyoyin sada zumunta da dama.

Rahotanni sun ce gwamnatin mulkin sojan ta kuma dauki irin wannan mataki a karamin ofishin jakadancin Faransa da ke Zinder, Tera, Oualam, Ayorou, Dosso, Yamai, Filingue da ko’ina.

Shugaban kwamitin tallafawa na kasa na CNSP Elh Issa Hassoumi Boureima, ya bukaci dukkan abokan huldar sansanonin Faransa da ke Nijar da su dakatar da duk wani nau’in mai na ruwa, wutar lantarki da kayayyakin abinci.

“Bugu da ƙari, duk abokan hulɗar da suka ci gaba da taimakawa Faransawa wajen samar da kayayyaki da ayyuka, za a ɗauke su makiyan mutane masu iko.”

Rahotannin na zuwa ne bayan wa’adin kwanaki biyu da gwamnatin mulkin sojan kasar ta baiwa jakadan Faransa Sylvain Itte na barin kasar ta Nijar.

Dangantaka tsakanin gwamnatin mulkin sojan Nijar da wasu kasashen yammacin duniya ciki har da kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta yi tsami tun bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli. Sai dai mahukunta a birnin Paris sun yi gaggawar yin watsi da umarnin da aka yi wa jakadan nata da yammacin ranar Juma’a, inda suka dage cewa Faransa ba ta amince da ikon shugabannin sojoji ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: