Shugabannin kasashen kudancin Afrika za su hada dubban dakaru don murkushe ta’addancin dake neman samun gindin zama a kasashensu.
Shugabannin kasashen dake kudancin Africa karkashin kungiyar SADC na gudanar da taron gaggawa a birnin Moputo domin tattaunawa kan barazanar ‘yan ta’addan dake neman samun gindin zama a kasashensu.
Tun a watan Afrilun da ya gabata aka tsare taron zai gudana, amma aka sauya lokacinsa saboda daidaita jadawalin wasu tarukan da shugabannin za su halarta.
Taron na yau na gudana ne a karkashin jagorancin shugaban kasar Africa ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Yayin taron shugabannin kasashen yankin na kudancin Afrika za su yi nazari kan kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta kunshi dakaru akalla dubu 3 domin murkushe mayakan na ‘yan ‘ta’adda, musamman a yankin Cabo Delgado dake kasar Mozambique.
‘Yan ta’adda sun kuntatawa sassan arewacin kasar Mozambique
A watan Afrilun da ya gabata wata cibiyar gudanar da bincike, hasashe gami da bada shawarwari kan lamurran da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma siyasa mai suna Pangea-Risk, ta ce mayakan ‘yan ta’adda na shirye-shiryen sake afkawa wasu yankunan arewacin Mozambique mai fama da hare-haren ta’addanci.
Kididdigar baya bayan nan dai ta nuna cewar mayakan da aka fi kira da Al-Shabaab, sun kashe dubban mutane, tare da tilastawa wasu akalla dubu 700 tserewa daga muhallansu, sakamakon hare-haren da suka kaddamar kan yankin arewacin Mozambique, musamman a lardin Cabo Delgado.