Shugabannin kasashe 27 sun amince da bayar da tallafin dala biliyan 50 ga Ukraine

0 236

Dukkan shugabannin kasashe membobin tarayyar turai 27 sun amince da bayar da tallafin dala biliyan 50 ga Ukraine bayan kasar Hungary taki amince da matakin.

Shugaba Voladymyr Zelensky ya yi maraba da matakin na kungiyar Tarayyar Turai, yana mai cewa hakan ma wani saƙo ne zuwa ga Rasha.

A cewar Zelensky tallafin kudaden zai taimakawa kasar wajen karfafa tattalin arzikin ta.

A cikin jawabin da ya yi cikin dare, shugaban ya ce matakin ya ƙara nuna yadda ƙasashen Yamma ke sauke nauyin da ya rataya kansu.

Ma’aikatar lura da harkokin tattalin arziki ta Ukraine tace tana tsammanin kashin farko na tallafin cikin watan Maris mai zuwa.

Ya ce Tarayyar Turai ta aiwatar da irin haɗin kan da ake buƙata, ƙasashe ashirin da bakwai sun dunƙule sun zama ɗaya. Sai dai akwai fargabar cewa firaminstan Hunagary zai ki amincewa da matakin kamar yadda yayi a babban taron na decembar bara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: