Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun ce an kwato kadarori na kimanin tiriliyan 1

0 266

Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun ce an kwato kadarori na kimanin tiriliyan 1 tun lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki a shekarar 2015.

A cikin wata sanarwa a yau, tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu; da memba a kwamitin rikon kwarya na APC, Barista Ismail Ahmed, da mai taimakawa shugaban kasa, Tolu Ogunlesi; da kuma Darakta-Janar na Kungiyar Gwamnonin APC, Salihu Lukman, sun ce an kwato kadarorin daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

A cewar sanarwar, ana aikawa da dukkan abubuwan da aka kwato domin amfani da su a Tsarin Gwamnati na Musamman da Shirye-shiryen Zuba Jari da Walwalar Jama’a ko a sanya su cikin kasafin kudin kasa na shekara-shekara.

Shugabannin na jam’iyyar APC sun ce baya ga kudaden da aka sace aka boye, gwamnatin Buhari ta kuma mayar da hankali kan tabbatar da cewa an kwato kudaden haraji da sauran basussukan da gwamnatin tarayya ke bi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: