Shugaban rundunar dakarun RSF ya sanar da tsagaita wuta domin bukukuwan sallah

0 329

Shugaban rundunar dakarun RSF ya sanar da tsagaita wuta da za ta fara aiki domin bukukuwan babbar sallar Idi da za a fara ranar Laraba.

An bayar da sanarwar dakatar da rikicin ne a wani sakon murya da aka watsa a gidan talabijin na Al Arabiya wanda shugaban kungiyar RSF, Muhammad Hamdan Dagalo, ya gabatar.

Ya ce matakin zai yi aiki ne a ranakun Talata da Laraba.

Muhammad Hamdan Dagalo, ya kuma yi Allah-wadai da cin zarafi da ake yi wa fararen hula – ciki har da wadanda sojojinsa ke yi. Ana zargin kungiyar ta RSF da aikata laifukan cin zarafin mutane a Darfur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: