Shugaban mulkin sojin Nijar ya sha alwashin bazasu sake komawa ECOWAS ba

0 347

Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sha alwashin cewa babu ɗaya daga cikin ƙasashen Sahel uku da suka yanke shawarar ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS da za ta koma cikin ƙungiyar.

Janar Tchiani ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da tashar labarai ta RTN a Yamai babban birnin ƙasar a jiya Litinin.

Sawaba radio ta rawaito cewa, hukumomin soji a Burkina Faso da Mali da kuma Nijar a ranar 28 ga watan Janairu, sun sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka cikin gaggawa.

Shugabannin kasashen uku sun fitar da wata sanarwa, inda suka ce shawarar da suka ɗauka ta barin ƙungiyar mai girma ce kuma ba tare da bata lokaci ba.

Da yake mayar da martani kan sakamakon janyewar ƙasashen daga ƙungiyar Ecowas a kan harkokin tsaro da kasuwanci da zamantakewa, Tchiani ya kara da cewa yanzu duniya a cure take wuri guda saboda haka ba sai da Ecowas kaɗai za su rayu ba, don haka, Allah zai ciyar da kowane ɗan adam da ya halitta.

Dan gane kuma da batun hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum, sai Janar Tchiani ya ce ba za su taba sakin Bazoum ba, domin sakin Bazoum ya yi daidai da daɓa wa kai wuka a ciki wanda hakan zai cutar da ‘yan Nijar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: