Shugaban Miyetti-Allah yayi kira da ana sanya Fulani makiyaya cikin taimakon da ake bai wa al’umma

0 254

Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti-Allah reshen jihar Kwara, Bello Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa suna son ganin an sanya Fulani makiyaya cikin taimakon da ake bai wa al’umma na rage radadin cire tallafin man fetur.

A lokacin da yake bayani ranar Lahadi, Abubakar ya ce an bar al’ummar Fulani a baya, wajen rabon kayan tallafi da aka soma bayarwa domin rage raɗaɗin talauci da ‘yan ƙasa ke fuskanta sakamamkon cire tallafin mai.

Shugaban ƙungiyar ta jihar ya koka a kan yadda kowane lokaci ba a bai wa Fulani cikakkiyar kulawa, inda ya ce galibinsu ma ba su da asusun ajiyar kuɗi a banki bale har su iya cirewa idan buƙatar hakan ta taso.

Ya ce a duk lokacin da za su kai dabbobinsu kasuwa sufuri kan kwashe kaso mai yawa na kuɗin dabbobin da aka sayar.

Abubakar Bello ya kuma roƙi gwamnati ta taimaki makiyaya da alluran rigakafin baƙin cutukkan da kan kashe musu dabbobi.

Ya gargaɗi ɓata gari a cikin Fulani da ke aikata munanan ayyuka da su yi watsi da ta’addanci tare da rungumar zaman lafiya.

Kana ya shawaraci manoma da makiyaya da su nemi hanyoyin tattaunawa tsakaninsu domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a cikin al’ummunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: