Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci iyayan yara da su tabbar cewa yayan su sun samu ilimi, tare da cewa kada su dauki hakan a matsayin wasa.
Shugaba Buhari ya bayyana hakane a wajan taron kasa da kasa dake gudana a birnin Landon, da nufin inganta ilimin duniya.
Shugaban kasar ya kara da cewa ya yarda cewa, hakika dukkannin yaro ko al’ummar da ta rasa ilimi to tayi babban rashi.
Shugaban Buhari yayi bayanin cewa girman kasa da kuma yawan al’ummar kasar nan yana daga cikin kalubalan da kowace gwamnati ke fuskantar a wannan fannin, sai dai gwamnati da kuma iyayan yara dukkannin su sun yarda cewa ilimi shine matakin farko na kowacce irin nasara.
Ya kara da cewa, dukkannin wanda ya rasa ilimi to hakika ya rasa komai, tare da cewa kasar nan tana sane da bawa bangarang ilimi fifiko, yayinda iyayan yara ke sadaukarwa wajan ganin cewa yayan su da kuma al’ummar su ta samu ilimi.
A wajan taron ya samu halartar shugabannin kasashen duniya da suka hada da Nana Akufo-Addo na Ghana, da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, Lazarus Chakwera na Malawi da sauran su.
Ko wanne shugaba yayi bayanin bangaran ilimi na kasar sa, da kuma yanda za’a kara samar da kasafin kudi, domin daidaita yanayin.