Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayi ga iyalan da ambaliyar ruwa ta rutsa da su

0 250

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayi ga iyalai da sauran wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su sakamakon ci gaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a makwannin da suka gabata.

Lamarin ya shafi dubban mutane a jahohi 32 na Najeriya, tare da haifar da asarar gidaje, gonaki, rayuka da rushewar rayuwa ta yau da kullum.

Shugaban, wanda ya koma aiki a ranar Laraba bayan kebewa na kwanaki biyar bayan balaguro zuwa Landan, ya nuna damuwa kan halin da ake ciki.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, a jiya Laraba a Abuja ya rawaito shugaban yana cewa a ko yaushe yana saka ido kan lamarin kuma za su tabbatar da duk wani taimako da za a iya bai wa wadanda abin ya shafa.

Shugaba Buhari, duk da haka, ya yi kira da a sami kyakkyawan hadin kai tsakanin hukumomin tarayya ciki har da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa da gwamnatocin jihohi don habaka al’adar girmama hasashen yanayi.

Sanarwar ta tunano yadda ambaliyar ruwa saman ya zanyo asarar gidaje da gonakai da kuma rayuwa masu tarin yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: