Shugaban kasa Bola Tinubu zai ware kudade domin gyaran hanyoyi a fadin kasar nan

0 297

Ministan ayyuka Dave Umahi, yace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai ware kudade domin gyaran hanyoyin a fadin kasar nan.

Dave Umahi, yace za’a maida hankali domin a tabbatar aikin ya tafi yadda ya kamata.

Tsohohn gwamnan jihar Ebonyi, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai fitar kudaden gyaran ayyukan.

Ya kuma kara da cewa, kudaden da za’a kashe ba gyaran kwalta kadai za’ayi ba.

A cewar Ministan ayyukan, wanda rantsar da shi ranar litinin din nan yayi alkawarin sake fasalin titin Lokoja zuwa Ajaokuta cikin makonnin biyu.

Ya kuma kara da cewa nan ba da jimawa ba aikin zai fara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: