Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya baiwa ministoci 45 mukamai da majalisar dattawa ta tabbatar a ranar Litinin.
Jerin sunayen ma’aikatun da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya sanar, ya nuna yadda aka raba wasu ma’aikatu tare da kirkiro wasu sabbi.
Wasu ma’aikatun kuma suna samun ƙarin ayyuka.
Sawaba radio ta rawaito jerin sunayen minstocin 45 da ma’aaikatunsu.
Babu tabbas ko shugaba Tinubu zai ci gaba da rike mukamin babban ministan man fetur.
Kamar yadda Magabacinsa, Muhammadu Buhari, shi ne ya kula da harkokin ma’aikatar a tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki.
A halin da ake ciki kuma, a ranar Litinin mai zuwa ne shugaba Tinubu zai rantsar da sabbin ministocin a babban dakin taro na fadar gwamnati, dake birnin tarayya Abuja da karfe 10:00 na safe. Kamar yadda Sakataren gwamnatin tarayya Dr George Akume ya bayyana haka a daren jiya a cikin wata sanarwa.