Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika da sabbin sunayen ministoci da Majalisar Dattawa za ta tantance su

0 443

A yau ne shugaban kasa Bola Tinubu zai aika da sabbin sunayen ministoci da majalisar dattawa za ta tantance su.

A cewar wata majiya mai tushe a majalisar dattawa, sunayen zasu zo jiya da daddare ko kuma da sanyin safiyar yau.

Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa za a karanta sunayen sabbin rukunin ministocin da za a tantance a zauren majalisar a yau laraba

Yau ne za a sa ran kammala tantance mutane 28 da aka mika sunayen su domin tantance su yayin da sauran kashin na biyu za a tantance nan gaba.

A ranar Litinin ne Majalisar Dattawa ta tantance 14 daga cikin 28 na Ministoci da Shugaban Kasa ya mika a baya yayin da aka tantance karin mutum 9 a jiya Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: