Shugaban kasa Bola Tinubu bayyana tallafin man fetur a matsayin damfara

0 348

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana tallafin man fetur a matsayin wata damfara da kuma tsarnaki dake shalatale kokarin ci gaban kasa, inda ya ce tallafin ta taimaki wasu kasashen waje wajen rage tsadar kayayyaki, da kuma ta’azzara ayyukan fasa kouri a cikin gida.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa, a cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan ayyuka, sadarwa, Dele Alake, ya fitar jiya.

Karon farko da yake jawabi ga ‘yan Najeriya a kasar Faransa, Tinubu ya bayyana cewa mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudi, Wale Edun da Alake ya cire batun tallafin man fetur daga jadawalin jawabinsa na farko, amma yana ganin ya dace a dakatar da tallafin a ranar farko.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban kasar ya yi tsokaci a bainar jama’a game da jawabinsa a ranar 29 ga watan Mayu, inda ya bayyana cewa “tallafin mai ya tafi”.

Wannan tsokaci dai ya janyo tashin farashin da kuma tabarbarewar al’amura, lamarin da ya kai ga kiran zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi.

Hakan dai na faruwa ne duk da matakin farko da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na kawo karshen biyan tallafin man fetur zuwa watan Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: