Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya caccaki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ka iya jefa shi cikin matsala a yunkurinsa na sake tsayawa takara a 2027.
Gabam ya lissafa cire tallafin mai ba tare da tanadi ba, daidaita kudin musaya, karin farashin wutar lantarki da na sadarwa a matsayin matakan da suka fi jefa al’umma cikin kunci.
Ya bukaci Tinubu da ya sake duba wadannan tsare-tsare tare da canza ministocinsa don ceto gwamnatinsa daga faduwa.
A cewarsa, irin gangamin da ake yi a yanzu yana kama da wanda aka yi a kan Jonathan a shekarar 2012, wanda ya hana shi sake cin zabe.