Shugaban ƙasar Senegal na shirin rusa majalisar dokokin ƙasar

0 169

Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye na shirin rusa majalisar dokokin ƙasar bayan da ƴan majalisar dokokin ƙasar mai rinjayen ƴan adawa suka ƙaryata ajandar gwamnatinsa na tsawon watanni, kamar yadda kafar yada labarai ta Faransa RFI ta ruwaito a jiya.

Ya zuwa yanzu, wata biyar bayan nasarar da ya samu a zaɓen Shugaban Ƙasa da aka yi a watan Maris na 2024, bisa doka ta amince shugaba Faye ya rusa majalisar.

Jam’iyyar shugaban dai na da kujera 23 ne kawai daga cikin 165 na Majalisar Dokokin ƙasar, wadda ƙawancen tsohon shugaban ƙasar Macky Sall ke iko da shi.

Tuni dai ƴan adawa suka toshe wasu ƙudirorin gwamnati, ciki har da lokacin muhawarar gabatar da Kasafin Kuɗin watan Yuni.

Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Amadou Mame Diop, ya bayyana goyon bayansa ga rusa majalisa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: