Shugaba Tinubu zai cike mukamai mafi yawa da mambobin jam’iyyarsa ta APC

0 370

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na shirin cike gibin mutane 2,000, biyo bayan rusa shuwagabannin hukumomin gwamnati sama da 153 a ranar Litinin.

A jiya laraba ne aka bayyana cewa Shugaban Kasar zai cike mukamai mafi yawa da mambobin jam’iyyarsa ta APC.

Rusassun hukumomin na daga cikin mutane 209 da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a watan Disambar 2017.

 An  ruwaito cewa, a daren ranar Litinin Shugaban ya sanar da rusa shuwagabannin hukumomin gwamnatin tarayya, hukumomi da kwamitoci.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar, ta ce kwamitocin da kansiloli ne kawai da aka jera a cikin jaddawali na uku, sashe na 153 (i) na kundin tsarin mulkin tarayyar na shekarar 1999. Majalisar Shari’a ta kasa, Ofishin da’a; Majalisar Jiha; Hukumar Halayen Tarayya; Hukumar Kula da Ma’aikata ta Tarayya; Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa; Hukumar Kididdiga ta Kasa; Hukumar Kula da ‘Yan Sanda; da hukumar Tattara Haraji da Hukumar Kuɗi, na daga cikin hukumomin da aka cire daga umarnin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: