Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da yawaitar sace-sacen mutane da hare-haren ‘yan bindiga, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin tada hankali, rashin tsoron Allah, da kuma mugun nufi.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Jam’iyyatu Ansaridden, wata kungiyar addinin islama a fadar gwamnati a ranar Talata a Abuja.
Shugaban ya ce yayin da hukumomin tsaro ke aiki tare don magance kalubalen da ake fuskanta, za’a kuma samar da kayan aiki, da kuma fitowa da tsare-tsaren da ake bukata don bunkasa ilimin matasan Najeriya.
Tinubu ya ce ilimi shi ne maganin matsalolin da ke haifar da tada hankalin al’umma, inda ya kara da cewa, “Babu wani makamin da zai yaki talauci da ya kai ilimi. Shugaban ya kuma jaddada bukatar inganta ingantaccen ilimi ta hanyar cibiyoyin koyar da ilimin addinin Islama ga matasa a Arewacin Najeriya don bunkasa ci gaba a yankin, Najeriya, da Afirka baki daya.