Shugaba Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaro na Najeriya

0 539

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya nan take.

Matakin na zuwa ne daidai lokacin da sabon shugaban ya sanar da amincewa da sallamar hafsoshin da ke jagorantar rundunonin tsaron ƙasar daga aiki.

Wata sanarwa da Mista Willie Bassey daraktan yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta bayyana Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro.

Tinubu dai ya naɗa Manjo Janar C.G Musa a matsayin babban hafsan tsaro, bayan sallamar Laftanal Janar Lucky Irabor.

Sai kuma Manjo Janar T. A Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, inda ya canji Laftanal Janar Faruk Yahaya.

Haka zalika, Rear Admiral E. A Ogalla ya zama babban hafsan sojin ruwa na Najeriya, inda ya maye gurbin Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.

Akwai kuma Air Vice Marshal H.B Abubakar a matsayin sabon babban hafsan rundunar sojojin sama na ƙasar, inda ya gaji Air Marshal Oladayo Amao.

Ƙarin manyan jami’an tsaron har da DIG Kayode Egbetokun a matsayin Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Usman Alƙali Baba.

Haka kuma sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya naɗa Manjo Janar EPA Undiandeye a muƙamin babban hafsan rundunar tattara bayanan sirri ta ƙasar wato Defence Iintelligence.

Sauran naɗe-naɗen da Shugaba Tinubu ya amince da su akwai Kanal Adebisi Onasanya a matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa.

Sai Laftanal Kanal Moshood Abiodun Yusuf a matsayin sabon kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa runduna ta 7 da ke Asokoro a birnin Abuja.

Haka zalika, an naɗa Laftanal Kanal Auwalu Baba Inuwa, kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa, runduna ta 177 da ke jihar Nasarawa.

Tinubu ya kuma naɗa Laftanal Kanal Mohammed J. Abdulkarim matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa, runduna ta 102, da ke Suleja a jihar Neja.

Yayin da Laftanal Kanal Olumide A. Akingbesote zai karɓi ragamar aiki a matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa, runduna ta 176 da ke Gwagwalada a Abuja.

Ƙarin manyan jami’an sojojin tsaron fadar shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya amince da naɗin su akwai Manjo Isa Farouk Audu a muƙamin kwamandan kula da dakarun atilare na fadar shugaban ƙasa.

Sai Kaftin Kazeem Koyejo Hamzat a matsayin kwamandan dakarun soji masu tattara bayanan sirri a fadar shugaban ƙasa.

Akwai kuma Manjo TS Adeola a matsayin kwamandan kula da makamai a fadar shugaban ƙasa, yayin da Laftana A Aminu zai kasance matsayin mai taimaka masa.

-BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: