Shugaba Tinubu da sarkin Qatar sun sanya hannu kan wasu alkawura da za su bude kofar inganta fannoni a Najeriya da Qatar

0 268

Shugaban kasa Bola Tinubu da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da za su bude kofar inganta muhimman fannoni tsakanin kasashen biyu.

Bangaren da yarjejeniyoyin za su shafa sun hadar da fannonin ilimi da kasuwanci da inganta zuba jari, da sama wa matasa ayyuka da harkar ma’adinai da yawan bude ido da wasanni.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce an cimma yarjejeniyar ce a fadar sarkin Qatar.

Shugaba Bola Tinubu ya ce a shirye kasarsa take don yin maraba da masu zuba jari, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi na inganta zuba jari a kasar.

shugaban kasar ya ce babban karfinsu shi ne mutanensu. karfinsu ya dogara kan matasansu. suna da karfi , da fikira da yarda da kansu.

Ya kara da cewa matasan kasar na da ilimi kuma suna da fikirar neman sana’a a duk inda take.

Shugaba Tinubu ya nada ministan kudi da na tattalin arziki, mista Wale Edun a matsayin wanda zai jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya da za ta tattauna da hukumomin Qatar wajen gano bangarorin da za a zuba jarin da aiwatar da shi, don ciyar da kasar gaba.

Shugaba Tinubu dai na ziyarar aiki a kasar Qatar tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: