Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi Alkawarin kara kasafin kudi a fannin Ilimi da kaso 50 cikin dari nan shekaru biyu masu zuwa.
Shugaba Buhari ya yi Alkawarin cewa, gwamnatinsa zata kara kudaden da take warewa fannin da kaso 100 nan shekaru 4 masu zuwa.
Kakakin Shugaban Kasa Mista Femi Adesina, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taro na shugabannin kasashen Duniya Mai taken ‘‘Kara yawan Adadin kudade a fannin Ilimi domin bunkasa fannin,’’
Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari ya sanya hannu kan wani daftari, a taron na birnin London, wanda yake nuna jajircewar Najeriya wajen bunkasa fannin.
A ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya tafi birnin London, domin halartar taron da Firaministan Burtaniya Boris Johnson da shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta suka shirya.
Ana saran taron zai hada shugabannin kasashen Duniya da sauran masu ruwa da tsaki wuri guda, domin lalubo hanyoyin bunkasa ilimi a kasashen.