Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan rikicin kabilanci.

0 206

Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan rikicin kabilanci dake faruwa a kasar nan, tare da cewa gwamnatinsa zata kare dukkannin kungiyoyin addinai dana kabilu, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999 ya amince.

Cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan kafofin yada labarai Malam Garba ya fitar a jiya Lahadi, yace Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa zata kare dukkannin mabiya addini, da kabilun dake kasar nan.

Shugaba Buhari ya gargadi irin wadannan kungiyoyin cewa gwamnatinsa ba za ta kyale su su ci gaba da rura wutar kiyayya da tashin hankali kan wasu jama’ar kasar ba.

Sanarwar ta kuma ce shugaban ya yi tir da rikce-rikicen kuma ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamantinsa za ta dauki matakan da su ka dace domin kawo karshen wadannan tashe-tashen hankulan da ke karuwa a cikin kasar.

Daga karshe shugaba Buhari, ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya da gwamnonin jihohi da sauran shugabanni na siyasa da jama’a su ka zaba daga sassan kasar, da su hada hannu da gwamnatin tarayya domin tabbatar da al’umomin da ke yankunan da su ka fito ba su basu tayar da rikici ba, saboda dalilai na bambancin kabila ko wasu dalilai kamar na bangaranci da na addini.

Leave a Reply

%d bloggers like this: