Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da gina barikoki ga ma’aikatan NDLEA

0 190

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gina barikoki ga ma’aikatan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan a jiya ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin ayyukan hukumar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban na NDLEA ya ce gina barikoki ga ma’aikatan hukumar ya zama wajibi don kare su da iyalansu daga masu aikata miyagun laifuka.

Marwa ya ci gaba da bayyana cewa ya nemi a dauki karin ma’aikata don baiwa hukumar damar gudanar da ayyukanta.

Dangane da ayyukan hukumar, Buba Marwa ya bayyana cewa hukumar ta kwace miyagun kwayoyi da suka kai sama da naira biliyan 100, yayin da aka ajiye kudaden da aka kwato daga hannun barayin miyagun kwayoyi a babban bankin kasa CBN.

Leave a Reply

%d bloggers like this: