Shugaba Kais Sa’eed na Tunisia, ya bayyana a bainar jama’a a jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasar bayan shafe makwanni biyu ba a san halin da ya ke ciki ba.
‘Yan adawa dai sun yi ta yaɗa jita-jitar cewa shugaban na cikin matsananciyar jinya.
A wani bidiyo da aka yaɗa a intanet, shugaba Sa’eed ya bayyana jita-jitar da ake yaɗa wa da cewa haukace tsagwaronta da makiya ke kitsawa domin tada hankalin al’ummar Tunisiya.
Sai dai a cikin bidiyon, Kais Sa’eeda ya yi ta yin tari akai-akai, ya kuma kare matakin da cewa mura da tari da ya ke fama da ita bai kai ‘yan adawa su fara kokarin maye gurbinsa ba.
Tun a shekarar 2021 shugaban ya ke jagorantar Tunisiya bayan ƙwace iko a bara, kuma ya yi amfani da karfin doka da bai wa ofishinsa karfin iko maras iyaka.
- Comments
- Facebook Comments