A yau ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki kasar Saudiyya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu, ya ce tafiyar ta tsawon kwanaki takwas ita ce ziyarar shugaba Buhari ta karshe zuwa kasa mai tsarki a matsayin shugaban kasa.
Garba Shehu ya ce kasancewar sa ziyarar aiki ta karshe da shugaban zai yi zuwa Saudiyya, zai yi amfani da damar da ya samu wajen gudanar da aikin Umrah.
Sanarwar ta kara da cewa zai samu rakiyar mataimakansa.
Shugaba Buhari wanda zai kammala wa’adi na biyu a mulki ranar 29 ga watan mayu, an fara zaben sa a shekarar 2015 bayan ya fafata da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Zaben da Jonathan dai ya amince da shan kaye kafin a kammala kidayar kuri’u. A ranar 29 ga watan Mayu ne ake sa ran za a rantsar da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, duk da cewa wasu jam’iyyun adawa na kalubalantar nasararsa a babban zaben da aka kammala.