Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koka kan tarin matsalolin tsaron da suka addabi sassan kasar duk da matakin rufe iyakoki na kan tudu da gwamnatinsa ta dauka, domin dakile kwararar makamai cikin kasar.
Buhari ya bayyana haka ne ranar jiya Juma’a a birnin Abuja, yayin taron kwamitin fadar shugaban kasa kan inganta tattalin arzikin Najeriya wanda ke karkashin jagorancin Farfesa Doyin Salami.
Shugaban Najeriyar ya jadadda cewar babban makasudin rufe iyakokin tudu shi ne dakile fasakaurin haramtattun kayayyaki, man fetur da kuma makamai, amma matakin bai yi nasarar dakile matsalar tsaron da Najeriya ke ciki ba.
A cewar shugaba Buhari tsaka mai wuyar da Najeriya ta tsinci kanta a ciki, na nuna cewar ba shakka akwai wasu miyagun mutane dake son durkusar da kasar ko ta halin kaka.
Daga karshe shugaban ya shawarci jagororin al’umma a dukkanin matakan mulkin kasar kama daga tarayya, Jihohi, kananan hukumomi da kuma mazabu, da su gaggauta sake nazari tare da daukar matakn da suka dace wajen warware matsalolin da ‘yan Najeriya ke ciki.