Shugaba Buhari Ya Yaba Da Aikin Dakarun Soji A Arewa Maso Yamma

0 228

Shugaban rundunar sojin kasa Lucky Irabor yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na farin ciki da ayyukan dakarun dake yaki da ta’addanci a arewa maso yammacin Najeriya.

Lucky Irabor ya bayyana haka yau, a Maiduguri lokacin da yake jawabi ga dakarun sa kai a Helkwatar su.

Babban hafsan sojin ya yaba da irin nasarar da dakarun ke samu, inda ya kara da cewa dakarun suna aiki bisa kishin kasa da sadaukarwa.

Irabor yace kwamandojin sun iya bakin kokarin su wajen fatattakar mayakan Boko dana ISWAP. Kazalika Irabor ya gana da sojojin da suka jikkata wanda suke kwance a asibitin sojoji na Maimalari.

Leave a Reply